Shirin gwamnatin tarayya na tallafawa kiwo da makiyaya na kara samun karbuwa saboda kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta ce ta gamsu da shirin da wasu ke kira RUGA kuma za a fara aiwatar da shirin a wasu jahohin Arewa.
Da yake jawabi Jim kadan bayan kammala taron gwamnonin Arewa a Kaduna, shugaban kungiyar kuma gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, ya ce kungiyar ta ma tattauna maganar magance barace-barace.
Lalong ya ce kungiyar ta amince da cewa tsarin zai taimaka wajen magance hauhawar rikicin manoma da makiyaya a Najeriya.
Sai dai duk da haka gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, ya ce gwamnoni na fama da matsalar rashin iko kan jami'an tsaro.
Gwamna Bello ya ce gwamnoni ba su da ikon ba jami'an tsaro umarni sai su ce sai sun nemo izini daga Abuja.
Shima dai gwamnan jahar Jigawa, Mohammed Abubakar Badaru, ya ce taron gwamnonin Arewan ya karfafi juna kan yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Facebook Forum