An fafata a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya wadda za'ayi a shekara ta 2018 a kasar Rasha.
Inda a yankin nahiyar kasashen Afirka, wace aka bata damar kawo kasashe biyar da zasu wakilce nahiyar a gasar ta cin kofin kwallon kafa ta duniya suma suka kammala wasanninsu inda aka bayyana sunan kasashe biyar da zasu wakilci nahiyar a gasar ta 2018.
A ranar Jumma'a da ta gabata 10/11/2017 kasar Algeria tayi kunnen doki 1-1 da Najeriya, Afirka ta kudu ta sha kashi daci 2-0 a hannun Senegal.
Sai ranar Asabar inda Zambiya da Kamaru suka tashi kunnen doki 2-2 , Kasar Gabon da kasar Mali, suma suka tashi kunnen doki babu ci tsakani , Morocco, ta doke Ivory Coast 2-0 ita kuwa Tunisia da Libya sun tashi babu ci Congo, ta lallasa Guinea, da kwallaye 3 da 1.
Ranar lahadi Kasar Congo tayi canjaras 1-1 da Uganda, Ghana 1-1 Egypt, Kasashe biyar da suka samu nasarar samun gurbin a gasar sune Tunisia, Nigeria, Morocco, Senegal, da kasar Egypt.
Facebook Forum