Rundunar ‘yan Sandan jihar Abia, ta damke shugaban wata kungiyar da ta shahara wajan yin garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa mai suna Prince Agorom.
Shi dai Agorom dubunsa ta cika ne bayan da ya yin garkuwa da wani abinkin da ya yi ta kafar sada zumunta ta Facebook, mai suna Ozoemelam, wanda ya gayyace shi domin halartar bikin ranar haihuwa a layin Ibegbulam a unguwar Omuma a garin Aba.
A lokacin da Ozoemelam, ya isa wurin bikin sai aka bukace shi da ya mika abubuwan da suke tare da shi har da wayar hannu daga bisani aka nakadamasa duka sai aka yi amfani da wayarsa inda aka bukaci Naira Miliyan biyar (N5M), daga babban yayansa.
Amma cikin dare sai Allah ya baiwa Ozoemelam, sa’a alokacin da wadanda suka yi garkuwa da shi suke shara barci sai ya samu ya tsere ya nufi ofishin ‘yan Sanda.
Kwamishinan ‘yan Sandan jihar ta Imo, Leye Oyebade, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shine shugaban kungiyar, Oyebade, ya kara da cewa rundunar sa na cigaba da farautar sauran ‘yan kungiyar.
Facebook Forum