Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya fadawa Muryar Amurka cewa akwai wata tattaunawa da kungiyar zata yi da Amurka amma dai ba a fitar da rana da kuma inda za a yi tattaunawar ba.
Mujahid yana mai da martani ne tare da watsi da rahotanni da ya kira na karya, cewa wakilan kugniyar mayakan sa kan suna shirin shiga wata tattaunawa da jami’an Afghanistan a Saudi Arabia a wata mai zuwa.
Wakilin Amurka na musamman mai shiga tsakani a Afghanistan, Zalmay Khalizad ya yi wata tattaunawa ta lokaci mai tsawo tsakanin kwanaki biyu a tsakiyar watan Disemba da wata babbar tawagar Taliban a birnin Abu Dabi, inda wakilan Saudi Arabi da na Pakistan da ma na kasar dake daukar nauyin tattaunawar suka halarta.
Facebook Forum