Shugaban kasar China Xi Jinping, ya ce yankin Taiwan da ke jan ragamar shugabancin kansa, ya cire batun neman ‘yancin gashin kai a Tunaninsa, ya kuma amince cewa yankin na Taiwan hade yake da kasar China.
Shugaban Xi ya jaddada wannan tsohon manufofin gwamnatin China kan yankin na Taiwan ne, a lokacin da yake jawabinsa na cika shekaru 40 da gabatar da wani muhimmin jawabi da ya kafa tarihi, wanda ya aike da sako ga al’umar Taiwan, ya kuma kawo aka fara samun huldar diplomasiyya tsakanin bangarorin biyu da ba-sa-ga-maciji.
Shugaba Xi ya kara da cewa, hukumomin Beijing na da burin samar da wata kofa ta sake hadewa da hukumomin Taipei, inda za a gudanar da sha’anin mulki a matsayin kasa daya, mai bin tsarin shugabanci biyu.
Sai dai ya yi gargadin cewa, China ba za ta ba da dama ga duk wasu masu yunkurin ballewa ba, kuma za ta yi amfani da karfin soji, domin tabbatar da an zauna a dunkule.
Facebook Forum