Shugaban Amurka Barack Obama yace abinda ya biyo bayan shekara goma da kawowa Amurka harin ta’adanci, ya nuna karfin halin Amurka.
Da yake magana a shirye shiryen cikar shekara 10 da kawowa Amurka wan nan hari da ya halaka kusan mutane dubu uku, shugaban na Amurkan yace Amurka ta sha mummunar bugu, amma sai ta mike da karfi fiye da na da, yace kasar ta Amurka ta lashi takobin kare ‘ya’yanta da kuma hanyoyin rayuwarta.
A cikin shekaru 10 nan an tafka zazzafan muhawararori kan yaki da zaman lafiya, tsaro da kuma ‘yancin walwala. Amma sabo da tsananinsu da kuma hanyoyi da muke warware wadannan banbance banbancen dake mutunta al’adunmu da tsarin Demokuradiyya, hakan yana nuna karfinmu.
A sassan Duniya da dama anyi bukukuwa na karrama wannan rana, a a birnin London Yerima Charles da PM David Cameroon tareda iyalan ‘yan inigla su 67 da suka rasa rayukansu a harin, sunyi bikin aza furanni. Papa Roma Benedict yayi addua ta musamman ga iyalan wadanda suka rasa dangi a harin daga nan yayi kira ga jama’a su nisanci tarzoma maimakon haka su dage kan ayyukan hada kan jama’a, shimfida adalci da zaman lafiya.
Haka ma anyi irin wadannan bukukuwa a Faransa, Hungary, Poland, da kuma jamhuriyar Check. Yara sun rike kyandir a ofishin jakadancin Amurka dake Beijing.
Muna da karin bayani bayan labaran Duniya.
An kuma kara daukan matakan tsaro musamaman a birnin New York da Washington saboda bayanan yunkurin kawowa Amurka wani hari a dai dai wannan lokaci da harin na farko ya cika shekaru 10.