Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kona Alkur’anin A Sweden Ya Janyo Bore Daban-Daban A Kasashen Duniya


Wasu 'yan kasar Indiya masu zanga-zangar kona Alkur’ani mai girma a Sweden
Wasu 'yan kasar Indiya masu zanga-zangar kona Alkur’ani mai girma a Sweden

Kona Alkur’ani mai girma da neman amincewa a ci gaba da zanga-zanga da ta hada da kara lalata karin litattafai masu tsarki ya jefa kasar Sweden a cikin halin tsaka mai wuya, tsakanin kokarinta na tabbatar da yancin fadin albarkacin baki, da mutuntawar da take yi wa addinan tsirarun al’ummar kasar.

Sabani kan manyan akidu ya dagula burin Sweden na samun shiga kungiyar kawancen tsaro ta NATO, fadadawar da ke bukatar gaggawa bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, amma tana bukatar amincewar daukakin manbobin kungiyar na yanzu.

Zanga-zangar kona Al-Qurani a Sweden
Zanga-zangar kona Al-Qurani a Sweden

Tun a bara Turkiyya ta dakile damar shigar Sweden cikin kungiyar, bisa dalilan da ta zayyana da suka hada da boren kin jinin Turkiyya da na kin jinin musulunci a Stockholm.

Zanga-zangar kona Al-Qurani a Sweden
Zanga-zangar kona Al-Qurani a Sweden

Sai ga shi a makon jiya wani kirista dan gudun hijirar kasar Iraqi ya kona Alkur’ani a wajen wani masallaci a Stockholm a yayin gudanar da sallar idin babbar sallah, aika-aikar da mutumin ya ce, tana bayyana yadda ya ke ji ne game da Alkur’ani.

Zanga-zangar kona Al-Qurani a Sweden
Zanga-zangar kona Al-Qurani a Sweden

Kona Alkur’anin ya janyo Allah wadai daga kasashen musulmi, da kuma bore dabam-dabam daga masu tsatstsauran ra’ayi, ya janyo mahawara a kasar ta Sweden game da iyakar fadin al’barkacin baki. A yanzu yan sandan Sweden sun ce sun karbi sabbin bukatun iznin gudanar da zanga-zanga daga daidaikun jama’a da ke son kona Al’kurani har ma da litattafan Attaura da Linjila.

Kasashen musulmi sun bukaci Sweden da ta sa doka, yayin da shugaban Pakistan Shehbaz Sharif ya yi kiran a yi zanga-zangar tabbatar da kare mutuncin littafi mai girma na musulmai a lokacin sallar Juma’a, yayin da majalisar dokokin Pakistan din za ta tattauna batun kone Al-qur’anin.

~Hauwa Sheriff

XS
SM
MD
LG