Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Marigayi Issa Hayatou


Marigayi Issa Hayatou
Marigayi Issa Hayatou

Tun daga kasar Kamaru, zuwa sassa daban - daban na duniya, ana ci gaba da nuna alhini da juyayi bayan rasuwar Issa Hayatou, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Africa (CAF) a birnin Paris na kasar Faransa a ranar 08 ga watan Agustan 2024.

Kwana guda ya rage Hayatou ya cika shekaru 78 da haihuwa a duniya.

An haifi Hayatou a garin Garuwa na kasar Kamaru a shekarar 1946, inda ya gudanar da karatun Firaimare ada na sakandare da ma na Jami'a.

Ya samu shaidar zama malami mai bayar da horon guje-guje a Jami'ar Yaoude a 1973.

Issah Hayatou, hagu tare da shugaban FIFA, Gianni Infantino (AP)
Issah Hayatou, hagu tare da shugaban FIFA, Gianni Infantino (AP)

Issa Hayatu, ya yi wasanni daban-daban, kama daga wasan kwallon kwando, da wasan tsere na mita 400 da na mita 800 da ma wasan kwallon kafa.

Tsakanin 1964 zuwa shekarar 1971, ya zama zakaran tseren mitoci 400 da 800 na kasar kasar Kamaru, abin da ya sa ma, ya wakilci kasarsa, a wassanin kasashen Africa a kasar Congo Brazaville a 1965, hasali ma, yana bugawa a kungiyar kasar Kamaru ta wasan kwallon kwando da kungiyar kwallon kafa ta Jami'a a wannan lokacin.

Ya soma rika mukaman wasanni a 1974 inda ya zama magatakardan kungiyar kwallon kafa ta Kamaru, a lokacin yana shekaru 28 har zuwa 1983.

Daga nan, ya rike mukamin Darekta na wasannin kasarsa, a ofishin ministan wasanni da matasa tsakanin shekara ta 1982 zuwa 1986, inda daga nan, ya zama mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru tsakanin 1984 zuwa 1986 kuma daga nan ne ya zama shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar Kamaru har izuwa 1988.

Issa Hayatou a shekarar 2017 (AP)
Issa Hayatou a shekarar 2017 (AP)

Hayatou, mamba ne, na kungiyar kwallon kafa ta Afirka tun shekara ta 1986, kamin ya ja ragamar kungiyar a 1987 bayan rasuwar shugaban ta dan kasar Ethipiya Ydnekatchew Tessema.

Tsakanin shekarun 1990 zuwa 2008, Hayatou, ya zama mamba na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, kamin ya yi rikon kwarya hukumar biyo bayan murabus din Sepp Blatter a 2015 zuwa 2016, inda ya shirya zaben hukumar da ya bai wa Gianni Infantino damar zama sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

A ranar 16 ga watan Maris 2017, da kuri'u 14 ne dan kasar Madagascar Ahmed Ahmed ya kai Issa Hayatou kasa a zaben shugaban hukumar kwallon kafa ta Africa CAF, abin da ya kawo karshen shugabancin kwallon kafa na Afirka daga hannun Issa Hayatou.

Daga Bisani, shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya nada shi a matsayin shugaban sashen bunkasa kwallon kafa na kasar Kamaru.

Issa Hayatou, hagu, da Sepp Blatter, tsakiya da Michel Platini, dama (AP)
Issa Hayatou, hagu, da Sepp Blatter, tsakiya da Michel Platini, dama (AP)

Abin tuni a nan shi ne, a 1984, Issa Hayatou ne, ya jagoranci takwarorinsa ‘yan wasa a wasannin Olympics na Los Angeles.

Kuma a lokacin da yake shugaban hukumar kwallon kafa na Afirka CAF, ya kawo sauye-sauye, da suka hada da canza wa mahalarta gasar kwallon kafa ta Afirka daga 8 zuwa 16, yayin da ya dage aka karawa kasashen Afirka gurube a a gasar kofin duniya na kwallon kafa daga 2 zuwa 5, da ma kawowa wasannin na kofin duniya a Afirka ta Kudu a 2010.

Haka ma an canzawa wasannin kungiyoyin kulob na Afirka sunaye, daga Kofin Zakaru a daya hannun zuwa Kofin Champions League, yayin da Kofin Kalubalen ya koma Kofin CAF.

Issa Hayatou ya rasu yanada shekaru 77 a duniya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG