Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Gabar Ruwa Da Kenya: Somaliya Na Kokarin Bi a Hankali


Shugaba Muhammad Abdullahi Farmajo
Shugaba Muhammad Abdullahi Farmajo

A yinkurinta na sassauta takkadar da ta barke tsakaninta da Kenya kan gaba da yankin ruwa, kasar Somaliya mai fama da matsalar al-Shabab, ta bayar da tabbacin cewa ba za ta yi gaban kanta na har sai Kotun Duniya ta yanke hukunci.

Gwamantin Somalia ta na kokarin ta inganta huldar diflomasiyya da ta yi tsami biyo bayan matakin da Kenya ta dauka na dawo da jakadanta daga Magadishu da kuma ba wa jakadan Somalia umarnin ya bar kasar.

Kasahen biyu dai na takaddama ne kan gabar ruwa.

A wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi da yamma, gwamnatin Somalia ta ce ita ba ta ba da wani waje a yankin da ake ta kaddama akai ga masu sayen filaye ba. Somaliya ta ce ba ta da wasu take-take na yin hakan, har sai an yanke hukunci kan takaddamar gabar ruwa tsakanin kasashen biyu da kotun kasa da kasa (ICJ a takaice) da ke Hague ke saurare.

Samaliya ta sake tabbatar wa Kenya cewa ba za ta dauki wata matsaya ba na yin ayyuka a gurin har sai kotu ta yanke hukunci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG