Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Cinikayya Tsakanin Amurka, India Ta Zafafa

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo yayin wani taron koli da aka yi tsakanin Amurka da India
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo yayin wani taron koli da aka yi tsakanin Amurka da India

Kwararru na ganin cewa, wannan rashin jituwa ta fuskar kasuwanci tsakanin Amurkan da India, zai iya shafar burin da kasashen biyu suka sa a gaba, na dakile karbuwar da China ke kara samu a kasuwannin duniya.

India ta kara kudaden harajin da take karba kan kayayyakin Amurka da ake shiga da su kasar, yayin da takaddamar cinikayya ke kara zafafa tsakanin kasashen biyu.

Wannan mataki na martani da Indian ta dauka, na zuwa ne kwanaki bayan da hukumomin Washington suka cire Indian daga jerin kasashen da ke da gatan yin cinikayya da Amurka ba tare da wata takura ba.

Takaddamar cinikayyar har ila yau na zafafa ne, gabanin wata ziyara da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo zai kai a kasar.

Amurka na son India ta ba kamfanoninta karin damar yin hadahada a kasuwanninta, ta kuma rage takunkuman cinikayya.

Kwararru na ganin cewa, wannan rashin jituwa ta fuskar kasuwanci tsakanin Amurkan da India, zai iya shafar burin da kasashen biyu suka sa a gaba, na dakile karbuwar da China ke kara samu a kasuwannin duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG