Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Ta Kunno Kai Tsakanin Shugaban Nijar da Kungiyar Alkalan Kasar


Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou

Ranar Juma'ar da ta gabata shugaban kasar Nijar Mahammadou Issoufou ya rantsar da sabon shugaban wata kotu Alkashim Alhada da wanda ya maye gurbinsa a kotun da ya baro wato ministan kudi Sedi Sidibe mako daya bayan da kukumar dake kula da nade nade alkalai ta kammala canzawa alkalai wuraren aiki.

To amma kungiyar alkalai ta soki wannan matakin da shugaban kasar ya dauka na nada ministan kudi ya zama shugaban kotun dake sa ido alkan yadda gwamnati take kashe kudi.

Malam Nuhu Abubakar mataimakin sakataren kungiyar alkalan yana ganin da lauje cikin nadi domin nada dan siyasa ya zama shugaban kotun da yake da ikon ya binciki yadda ma'aikatar kudi ta kashe kudin gwamnati.

Yace an kai miinistan ya zama alkalin kotun da zai binciki yadda ya kashe kudin gwamnati a ma'aikatar da yayi aiki, inda ya zama minista. Shi ne wai yanzu zai binciki bin kaidar kashe kudaden da aka kashe yayinda yake ministan kudi. Ya zama malamin shari'a kuma shi ne abokin rigima, wanda zai binciki aikin da shi kansa yayi. Yace sun yi allawadai da nadin.

Kungiyar alkalan ta kira ga shugaban kasa ya janye wannan nadin. Yace idan shugaban kasa bai sauraresu ba zasu kirkiro da wata dabara. Duk wasu alamura na shari'a zasu tsaya. Zasu kai kara ga hukumomin kula da shari'a na duniya.

Amma ministan shari'a Umorou Ahmadou yace kowa na iya furta albarkacin bakinsa amma gwamnati ba zata ja da baya ba saboda cancantar wadanda aka nada.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG