Sabon matakin da hukumar zaben Najeriya, INEC, ta dauka na sanar da sakamakon zabe da na'ura mai kwakwalwa ko ta tauraron dan Adam tun daga rumfar zabe ba zai hana cika sakamakon kan takarda kamar yadda aka saba ba.
Jami'in yada labaran hukumar, Aliyu Bello, ya ce yin amfani da na'urar wani karin inganci ne akan abun da aka yi a baya.
Ya kuma ce za'a tabbatar da wadatattun batura ko na'urorin wuta domin kaucewa samun cikas a fannin wutar lantarki.
A cewar Aliyu Bello hukumar ta ga ya dace a yi amfani da kafofin zamani domin jami'in zabe ya aika da sakamakon daga rumfunar zabe kafin ma ya kai takardunsa.
Sai dai tuni masana a harkar zabe suka fara bayyana ra'ayinsu kan wannan sabon mataki.
Saurari abin da Alhaji Musa Muhammad Gidado Garba Gana, wani mai fashin baki ya ce dangane da wannan sabon tsari a wannan rahoto da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum