Bayan da Hukumomi a Najeriya, su ka amince da kafa kungiyar tsaro ta “AMOTEKUN” da wasu jihohin kudu maso yammacin kasar suka yi, Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya jagoranci taron yanke matsayar cewa gwamnonin su koma jihohinsu don a tsara doka a majalisun su don ayyukan rundunar su zama bisa doka.
Batun kafa rundunar ta “AMOTEKUN” ya jawo muhawara mai zafi musamman daga al’ummar arewacin Najeriya da ke ganin tamkar yankunan na Yarbawa na neman ware kansa ne a kaikaice daga sauran sassan kasar.
Shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma, Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya ce, an umarce su, da su koma don tsara dokar rundunar ta “AMOTEKUN”.
Alhaji Awaisu Giwa Kuta ya nuna takaicin ba da damar gudanar da rundunar da ya ce, hakan zai iya kawo rabuwar kan ‘yan Najeriya.
Kamar daukar mataki makamancin hakan su ma gwamnonin arewa ta tsakiya sun yi taro don kaddamar da rundunar da su ka ce ta ‘yan sandan cikin al’umma ne, wato ‘yan kato da gora masu mutunta sarakuna.
Gwamna Abdullahi Sule na Nassarawa ya kare muradin rundunar.
Saurari cikakken rahoton wakilin muryar Amurka, Nasiru Adamu El-hikaya.
Facebook Forum