Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan-Najeriya Na Taka Rawa Wajen Binciken Lafiya A Duniya


Likita Sagir Muhammad
Likita Sagir Muhammad

Dr. Sagir Muhammad, matashin likita ne daga jihar Kano a Najeriya, wanda yanzu haka yake karatun digiri na biyu a bangaren ilimin lafiyar al'umma a jihar Texas ta kasar Amurka. Ya samu damar kammala karatun firamare a garin Bichi, wanda ya samu damar shiga makarantar sakandire ta gwamnati da ke Gwale da kuma kwalejin kimiyya da fasaha ta jeka ka dawo a garin Kano. Ya samu damar shiga jamiar Bayero ta Kano bayan samu sakamakon jarrabawa mai kyau, wanda hakan ya bashi damar cimma burin shi na karatun likita.

Ya kammala karatun likita a shekarar 2010, hakan shine ya bashi damar bada gudunmuwar shi a harkar aikin kiwon lafiya a asibitoci da dama wanda suka hada da Federal Medical Centre Azare, National Eye Centre Kaduna, Aminu Kano Teaching Hospital, da kuma Sankara Comprehensive Health Centre.
Wannan matashin likitan yanzu yana karatu a jami'ar Texas A&M University, kuma yana aiki tare da farfesan ilimin kwayoyin cututuka a matsayin mataimakin mai bincike. Ya bayyanar da cewar bai samu matsala ba tun zuwan shi kasar Amurka. Yana fatan cigaba da karatun shi har zuwa digirin digirgir, duk a bankagaren binciken ilimin maganin ciwon zuciya bayan kammala digirinsa na biyu.

Dr. Sagir, ya bayyanar da karatun koyon aikin likitanci a matsayin karatu da ya fi kowane karatu sauki, idan dai mutun ya maida hankali da kuma kokarin fahimtar abun da aka koya mishi. Yana ganin babu wani karatu da yake da sauki a duniya, babban dai abun da ya kamata matasa su, sa a ransu shine za suyi kowane irin karatu don taimakon kan su da cigaban kasa baki daya, hakan da kuma naci wajen ganin sun fahimci karatu. Wannan shine sirrin kowane karatu a duniya a ganin likita Sagir.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG