Shugaban yayi wannan furuci ne lokacinda ya gana da Prime Ministan Belgium Charles Michel a birnin Brussels. Yace Amirka da kungiar NATO zasu yi aiki akan matsaloli dabam dabam, kuma yayi nuni da harin ta’adanci da aka kai Britaniya a ranar Litinin ya kuma lura da cewa batun ta’adanci ne ke kan gaba a ajandar shawarwarin da zasu yi.
Tunda farko shugaban na Amirka yace, ya kuduri aniya fiye da kowane lokaci na ganin cewa an samu zaman lafiya a duniya. Yayi wannan furucin ne bayan ya zanta da paparoma Francis a fadar Paparoman dake birnin Rome.
Fadar shugaban Amirka tace shugabanin biyu sun tattauna yadda addinai zasu iya magance bonen da bani Adama ke sha a kasashe kamar Syria da Libya wuraren da ‘yan kungiyar ISI ke iko da su.
Facebook Forum