Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Kashe Tsohon Saurayinta Da Hadin Bakin Sabon Saurayinta


Marigayi Abba Abbey.
Marigayi Abba Abbey.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta kama tare da tsare wani saurayi da budurwarsa da kuma wasu mutane akalla 5, da ake zargi da laifin kisan gilla ga wani Abba Abbey da ke unguwar Gidan Haki a tsakiyar birnin Sokoto.

Abba Abbey, wanda mataimaki ne na musamman ga tsohon gwamnan jihar, kuma dan majalisar Dattawa mai wakiltar Sokoto ta tsakiya Aliyu Magatakarda Wamakko, ya gamu da ajalinsa ne a daren Alhamis, washe garin Juma’ar da ta gabata.

Wasu majiyoyi masu kusanci da marigayin, sun shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, ana zargin tsohuwar budurwar sa ce ta hada baki da sabon saurayinta, suka sace Abbey, “inda daga karshe suka kashe shi, suka kuma jefar da gawarsa a kan titin Sokoto zuwa Durbawa, da ke yankin karamar hukumar mulkin Kware.”

Karin bayani akan: Abba Abbey, Aliyu Magatakarda Wamakko, jihar Sokoto, Nigeria, da Najeriya.

A cewar majiyar, budurwar mai suna Fatima Binta Riskuwa, ta yi soyayya da marigayi Abba Abbey, inda har suka yi niyyar aure a tsakaninsu.

To sai dai kuma daga baya sun rabu tun kafin a kai ga yin auren, inda Fatima ta kuma yin sabon saurayi mai suna Umar Abubakar.

“Fatima da sabon saurayinta Umar sun kuduri aniyar yin aure, to amma kuma tana fuskantar matsalar rashin kudi ne, shi ne ya sa ta tuntubi tsohon saurayinta Abbey, domin ya taimaka mata da kudin da zata yi auren” a cewar majiyar.

“To amma Abbey ya nuna mata cewa bai rike da kudi a lokacin, lamarin da ya sa ta shirya da sabon saurayinta, domin su sace marigayin, su kuma neni ya biya kudin fansa,” majiyar ta ci gaba.

Majiyoyin sun bayyana cewa Fatima ta kira Abbey ta wayar salula a daren na Alhamis, inda ta bukaci su hadu a wani kantin sayar da kayayyaki da ke unguwar Mabera.

Marigayi Abba Abbey
Marigayi Abba Abbey

“Da ya je sai ya tarar da ita tare da wani saurayi, wanda ta ce masa dan uwanta ne, ta kuma bukaci da ya kai su wata Unguwa. Bayan ya dauke su a motarsa, ya kai su a wani lungu ya ajiye su, yana kokarin fitowa da baya ne sai ya ga wata mota ta rufe shi ta baya, nan take kuma sai wasu suka fito rike da bindiga kirar AK-47, inda daga nan suka yi awon gaba da shi.”

An tsinci gawar Abbey ne a washe garin ranar Juma’a, bayan da aka kashe shi.

To sai dai kafin nan, rahotannin sun bayyana cewa Abbey ya yi ta kiran wasu mutane da yake hulda da su a daren da aka sace shi, yana neman su ba shi aron kudi naira miliyan biyu domin ya fanshi kan sa daga masu satar mutane, to amma ba inda aka dace ya sami kudin.

Bincike ya nuna cewa wadanda ake zargin sun bukaci ya biya naira miliyan 2, bayan sun gane cewa bai da kudi a asusunsa na banki da suka bincika ta wayar salularsa.

To sai dai a cewar wata majiya, sun yanke shawarar kashe shi ne bayan da suka kasa samun kudi a hannunsa, ta hanyar kakkarya gabobin jikinsa, da kuma taka shi da mota.

Wata majiya ta kusa da ‘yan sanda ta ce an sami cafke Fatima ne ta hanyar lambar wayar salularta, wadda ita ce ta karshe da ta yi ta kiransa a daren da lamarin ya auku, wanda hakan kuma ya kai ga kama saurayinta Umar, da wasu mutum 5.

Sallar Jana'izar Marigayi Abba Abbey
Sallar Jana'izar Marigayi Abba Abbey

Marigayi Abba Abbey yana da aure da 'ya'ya 5.

Yanzu haka kuma ‘yan sanda na ci gaba da bincike akan lamarin, a yayin da rahotannin ke bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin suna asibiti, sakamakon raunin harbi da suka samu a lokacin musayar wuta da ‘yan sanda, sa’adda ake kokarin kama su.

Sanata Aliyu magatakarda Wamakko a wajen ta'aziyyar marigayi Abbey
Sanata Aliyu magatakarda Wamakko a wajen ta'aziyyar marigayi Abbey

Tuni kuma da aka yi jana’izar marigayi Abba Abbey a masallacin Shehu Danfodiyo da ke Sokoto, kuma ta sami halartar tsohon gwamna kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta tsakiya, Aliyu Magatakarda Wamakko.

Wannan lamari ya haifar da fargaba a zukatan jama'a a jihar, ganin cewa ayukan satar mutane ka kuma kisan jama'a ya fara kai wa a babban birnin jihar.

Jihar ta Sokoto dai na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda ayukan 'yan bindiga da suka hada da kai hare-hare da kisan jama'a da kuma satar mutane domin karbar kudin fansa suka zama ruwan dare.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG