Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu Na Shirin Kaddamar Da Takardun Kudinta


Shugabannin Sudan ta Kudu da ta Arewa wato Salva Kiir da Omar al-Bashir a filin jirgin saman Juba
Shugabannin Sudan ta Kudu da ta Arewa wato Salva Kiir da Omar al-Bashir a filin jirgin saman Juba

Autar kasar duniya, wato Sudan ta Kudu, ta yi shelar cewa tana kan shirin bullo da takardun kudinta.

Autar kasar duniya, wato Sudan ta Kudu, ta yi shelar cewa tana kan shirin bullo da takardun kudinta.

Kudin ‘fan’ na Sudan ta Kudu zai kasance ne dauke da siffar John Garang, marigayi gwarzon fafatukar nemar ‘yancin kasar. Kudin zai fara isowa daga Burtaniya ta jirgin saman daukar kaya daga gobe Laraba, sannan a fara amfani da shi ran Litini mai zuwa.

Ministan Kudi David Deng Athorbei ya gaya wa manema labarai a Juba, babban birnin kasar, cewa za a biya albashin ma’aikatan gwamnati na watan Yulin nan ne da sabon kudin, wanda y ace zai kasance da kwatankwacin darajar kudin ‘fan’ din Sudan na yanzu.

An yi ta bukukuwa a birnin Juba ran Litini a daidai lokacin da ministocin gwamnatin kudancin Sudan da ta kasance da ‘yar kwaryakwaryar ‘yancin gashin kai su ka dau rantsuwa a kan mukaman da su ke a kai amma a matsayin na wucin gadi.

Da yammacin ran Litini din kuma Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri’ar janye sojojin kiyaye zaman lafiyan da aka tura Sudan su sa ido kan yarjajjeniyar zaman lafiyar 2005 da ta kawo karshen yakin basasar Sudan.

Sakatare-Janar na Majalisar dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya kasa shawo kan gwamnatin Arewacin Sudan ta amince sojojin kiyaye zaman lafiya su cigaba da zama saboda sauran abubuwan da ba a cimma maslaha a kansu ba. Da gwamnatin Amurka da na Burtaniya sun ce sun yi takaicin kada kuri’ar janye dakarun kiyaye zaman lafiyan.

XS
SM
MD
LG