Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Spain Za Ta Killace Wadanda Suka Shigo Daga Kasashen Waje


A yunkurin dakile shigo da sabbin masu cutar coronavirus, kasar Spain ta bukaci a killace wadanda su ke shigowa kasar daga kasashen waje na tsawon makonni biyu.

Kasar ta fara sassauta umarnin hana zirga -zirga na tsawon makonni bakwai da ta ayyana, bayan ta shiga jerin kasashen da cutar COVID-19 tafi tsanani a duniya.

Umarnin da ma’aikatar lafiya ta fitar a yau na nuni da cewa, ranar jumma’a za'a fara aiwatar da dokar killace mutanen da suke shiga kasar, kuma za ta shafi baki da kuma ‘yan asalin kasar Spain da suke komawa gida.

Za a kyale mutanen su je sayen kayan abinci ne kadai ko kuma kula da lafiyarsu cikin kwanaki goma sha hudun da aka killace su.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG