Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Iya Samun Karin Masu Kamuwa Da COVID-19 - Moon


Shugaban Koriya ta kudu, Moon Jae-in
Shugaban Koriya ta kudu, Moon Jae-in

Koriya ta Kudu ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a sake samun barkewar masu kamuwa da cutar COVID-19 a karo na biyu.

A ranar Lahadi, Shugaba Moon Jae-in ya fadawa ‘yan kasar cewa, “har yanzu akwai sauran aiki a gaba,” yayin da aka samu rahoto kan sabbin wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus, adadin da ba a taba gani ba cikin wata guda.

Karin bullar cutar ya zo ne a daidai lokacin da Koriya ta Kudu ta fara sassauta wasu dokokin da aka saka don dakile yaduwar cutar, ciki har da buɗe shagunan sayar da barasa da gidajen rawa.

Koriya ta Kudu ta rufe gidajen rawa da sauran wuraren harkokin yau da kullum sama da 2,100 a birnin Seoul, bayan da aka alakanta sabbin masu kamuwa da cutar da wadanda ke yawan zuwa gidajen rawa a karshen mako.

Yawancin wadanda suka kamun, sun samo asalin cutar ne daga wani mutum mai shekara 29 wanda ya shiga wasu gidajen rawa uku kafin daga bisani aka gano yana dauke da cutar.

Gabanin hakan, an yi niyyar bude makarantu a Koriya ta Kudun a wannan makon, amma mai yiwuwa a jinkirta yin hakan, bayan da aka samu barkewar cutar.

Hukumomin sun ce binciken da za a gudanar kan bullar sabbin masu dauke da cutar, shi zai nuna mataki na gaba da za a dauka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG