Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia Na Neman a Cire Mata Takunkumin Sayen Makamai


Shugaban Somalia Mohammad Abdullahi Mohammad (daga hagu) da Sarkin Saudi Arabia (daga dama)
Shugaban Somalia Mohammad Abdullahi Mohammad (daga hagu) da Sarkin Saudi Arabia (daga dama)

Domin magance matsalar hare-haren 'yan kungiyar Al Shebab, hukumomin Somalia sun yi kira ga kasashen duniya da a taimaka a cire musu takunkumin sayen makamai da aka kakabawa kasar.

Gwamtin Somalia na ci gaba da magiyar neman kasashen duniya su cire mata takunkumin sayen makamai da aka saka mata, yayin da ta ke ci gaba da fuskantar barazanar ‘yan kungiyar Al shebab.

Yayin da ya gabatar da jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma’a, fira ministan kasar, Hassan Ali Khaire, ya yaba da irin ci gaban da kasar ke samu ta fannin siyasa da kuma tsaro, inda ya yabi dakarun hadin gwiwa na tarayyar Afrika da ake kira AMISOM a takaice.

Fira ministan ya kara da cewa suna bukatar makamai a gurguje, saboda haka akwai bukatar a dage musu takunkumin sayan makaman domin dakarunsu su samu kayan fada da kungiyar ta Al shebab.

Ya kuma kara da cewa kasar a shirye take ta yi aiki da kasashen duniya domin a shata hanyar da za dage mata takunkumin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG