A Somalia, yawan wadanda suka halaka sakamakon mummunar harin bam da aka yi amfani da motar dakon kaya a Mogadishu, ya haura zuwa mutum 230, kamar yadda mukaddashin kakakin majalisar dokokin kasar Abshir Mohammed Ahmed ya gayawa Muriyar Amurka.
Mutane fiyeda 200 suka jikkata, ciki harda wakilin Muriyar Amurka.
Shugaban kasar Mohammed Abdullahi Farmajo, yace kasar "zata yi zaman makoki na kwanaki, domin jimamin rayukan d a suka salwanta na mutane da basu aikata laifin komi ba, ha kazalika, za'a sauke tutocin kasar kasa-kasa, domin nuna alhini."
Hakan shugaba Farmajo yayi kira ga 'yan kasar su hada kai sunyaki ta'addanci, yana cewa "lokaci yayi da ya kamata mu hada kai mu addu'o'i tare. Ta'addanci ba zai sami nasara ba."
A jiya Asabar ne aka kai harin a mararrabar hanyoyi da ake kira Zobe da ake yawan zirga zirga akai a Mogdishu babban birnin kasar.
Facebook Forum