A wani taron manema labarai da bangaren Bamanga Tukur suka kira sun ce ya zama wajibi su dauki matakin korar gwamnan jihar Murta Nyako daga jam'iyyarsu ta PDP domin take-taken gwamnan da masu goyon bayansa na neman canza sheka zuwa wata jam'iyyar.
Bayan gwamnan wadanda barazanar ta shafa har da mataimakinsa Barrister Bala Ngilari da 'yan majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi da wasu kusoshin jam'iyyar. Sakataren bangaren Bamanga Tukur ya ce su ba zasu yarda su bar wadanda aka zabesu a karkashin PDP su rika anfani da mukaminsu da kudin PDP suna cin zarafin jam'iyyar. Maimakon su yiwa talaka aiki sai suna yiwa jam'iyya zagon kasa. Ta dalilin haka ya zama wajibi su dauki matakan fatartakarsu daga jam'iyyar.
A nasu martani da suka mayar shugabannin PDP 'yan bangaren Kugama dake dasawa da gwamna Nyako sun yi fatali da barazanar suna cewa kuararin haramtattun shugabanni ne domin haka basu da matsaya ko madogara.Sun kara da cewa ba'a zabesu ba kuma haka rahoton Sule Lamido ya nuna.
Shi kuma gwamna Murtala Nyako ya ce yana nan daram cikin jam'iyyar PDP.
Ga rahoton Abdulawahab Mohammed.