Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Myanmar Sun Yi Niyyar Kisan Kare Dangi Ma Kabilar Rohingya - Rahoton MDD


Sojojin Myanmar A Jihar Rakhine
Sojojin Myanmar A Jihar Rakhine

Wata tawagar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar cewa sojojin kasar Myanmar sun yi niyar aiwatar da kisar kare dangi ne a kan kabilar Musulmin Rohingya, a lokacin da suka kora dubban daruruwan ‘yan kabilar daga kasar a cikin shekarar 2017.

Rahoton da tawagar ta fitar a jiya Alhamis ya kuma ce gwamnati ta gaza tabbatar da alhakin da ya rataya a wuyanta karkashin dokar kasa da kasa ta kisan kare dangi da gudanar da bincike da kuma hukunta masu laifin aikata kisan kare dangi.

Wani masani a cikin tawagar bincike, Radhika Coomarasawamy, ya fada yayin fitar da rahoton cewa, ayyukan cin zarafin bil adama da aka sa su bincika, laifi ne da yakamata a dorawa ma’aikatar sojin Myanmar ta “Tatmadaw”.

Sama da ‘yan kabilar Rohingya dubu dari bakwai ne suka arce daga jihar Rakhine ta Myanmar tsakanin watannin Agusta da Satumban shekarar 2017, biyo bayan hare hare da ‘yan bangar Rohingya suka kaiwa jami’an tsaro, lamarin da yayi sanadin mayar da martani daga sojoji. Sun ci gaba da neman matsugunai a sansanonin ‘yan gudun hijira a makwabciyar kasar Bangladesh.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG