Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tace Zata Yarda Da Wani Shirin Tsagaita Wuta A Syria


Wani babban jami’in diplomasiya na Rasha yace Rasha ba zata kara yarda da wani shirin tsagaita wuta da sunan barin kayan agaji su shiga birnin Aleppo na Syria da yaki ya daidaita ba.

A jiya Litinin ne Na’ibin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov yake wannan bayanin, bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta na awa 72 ta kare, inda kuma nan take jiragen yakin Rasha da Syria suka koma ga kai hare harensu.

Rasha da Syriar dai sun nace cewar suna kai hare haren nasu ne a kan ‘yan jihadi, a yayid da masu lura dda wainar da ake toyawa hade da kuma gwamnatocin yammacin duniya ke ganin hare haren cewa fararen hula ne kawai ake aunawa, yayinda suke dada fuskantar wahaloli iri-iri.

Wannan abu ya tilasta jami’an MDD su janye anniyarsu ta kwashe dimbin mutane birnin, saboda bangarorin dake yaki da juna basu bada tabbacin tsaron ma’aikatar kiwon lafiya ba.

Sojojin Syria da Rashan sun bude wasu farfajiyoyi guda takwas da fararen hula zasu yi amfani dasu su fice daga birnin.

Amma shakku da rashin amincewar da ake nunawa ga sojojin Syria da na kawarta Rasha ya sa fararen hula ko yan tawayen kadan ne suke yarda suyi anfani da da lafawar da aka samu wajen ficewa daga birnin.

XS
SM
MD
LG