A karo na biyu cikin wannan shekara, sojoji a kasar Ivory Coast sun rufe hanyoyi jiya juma’a a birane da dama na kasar domin yin zanga zangar nuna rashin amincewa akan rashin biyansu albashin su.
An fara tunzuri ne a Bouake, sa’anan ta bazu zuwa birnin Abidja da sauran biranen kasar. Anji karajin harbe harbe a baban sansani sojan kasar dake birnin Abija a yayinda sojoji suka ta harbi cikin iska.
Sojoji suna zanga zangar ce akan jinkirin da aka samu wajen biyansu alawus da gwamnati tayi musu alkawari bayan sunyi bore makamancin wannan a watan Janairu.
Gwamnantin kasar ta biya wani bangare na alawus din amma ta jinkira biyan sauran a saboda faduwar farshin coco, babar hajjar da kasar take sayarwa kasashen waje.
Anyi zanga zangar ce kwana daya, bayan wani mai magana da yawun soja ya nemi gafarar shugaban kasar Alassane Ouattara a saboda boren da sojoji suka yi a watan Janairu.
Facebook Forum