Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe Mutumin Da Ake Zargi Da Kitsa Harin Omoku


Dakarun Najeriya
Dakarun Najeriya

Dakarun Najeriya sun ce sun yi nasarar kashe shugaban wani gungun da ya shahara wajen yin garkuwa da mutane wanda ake zargi da shirya kisan garin Omoku na jihar Rivers a ranar sabuwar shekara.

Rundunar sojojin Najeriya da ke shiyya ta 6 a Birnin Fatakwal na jihar Rivers, ta tabbatar da halaka mutumin da ake zargi da kitsa harin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a garin Omoku kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.

Kwamandan rundunar sojin yankin, Major General Enonbong Udoh, ya tabbatar da kashe Johnson Igwedibia wanda aka fi sani da Don Waney.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da aka baje gawar Don Waney ga manema labarai hade da wasu gawarwaki biyu na ‘yan kungiyarsa a Birnin Fatakwal.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Don Waney, kamar yadda jami’an tsaron yankin suka bayyana, gawurtaccen mai yin garkuwa da mutane ne.

Kwamandan ya kara da cewa,har ila yau an kashe mataimakin Don Waney, Ikechukwu Adiele, wanda shi ya jagoranci kisan da aka yi a Omoku a ranar sabuwar shekara.

Ya kara da cewa, bayan da suka aikata kisan na Omoku ne suka koma Birnin Enugu, inda suka kama haya domin bat da kama.

Amma da taimakon rundunar soji ta 82 da ke Enugu aka yi kokarin cafke mamatan, a cewar sojojin.

Hakan ya sa suka yi yunkurin yin artabu da dakarun na Najeriya, abinda da ya sa aka bindige su har lahira kamar yadda jaridar ta daily Trust ta wallafa a shafinta na yanar gizo a yau Lahadi.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG