Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji sun ce mutane 55 sun mutu, an sako fursunoni 105, a harin da ‘yan Boko Haram suka kai kan garin Bama

Wasu mutanen da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne dauke da muggan bindigogi sun kai farmaki talata a kan garin Bama dake arewa maso gabashin Najeriya, suka sako fursunoni sama da 100, da haddasa mutuwar mutane 55, a cewar jami’an Sojan Najeriya. Wadannan hare-haren masu kaifin kishin Islama dauke da muggan makamai, sune na baya-bayan nan a ire-irensu dake kara yin muni tare da barazanar kawar da zaman lafiya a kasar da ta fi kowace kasa yawan jama’a a nahiyar Afrika. An kai hare-haren a wurare da dama a garin Bama dake jihar Bornon Najeriya, wajenda harbe-harbe da fashe-fashen boma-bomai ke cigaba babu kakkautawa tun bayan da kungiyar ta dauki makamai a shekara ta 2010. A daya daga cikin mafiya girma da aka gani a Najeriya, mayakan sun kai wa wani babban kurkukun kasa hari shima, a inda suka sako mutane 105 a cewar jami’an gwamnati.

XS
SM
MD
LG