Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji na Zargin Masallaci da Boye Makamai


Sojojin Najeriya (File Photo).
Sojojin Najeriya (File Photo).

An binciki masallaci da gidan liman a Jihar Abia.

Jami’an tsaro sojojin Najeriya, sun kama wani Limamin Masallacin Jumu’a da wasu shuwagabani su goma sha uku a garin Aba na jihar Abia, bisa zargin su da boye wasu dimbin makamai.

An kama mutanen nea wani samame da rudunar soja Najeriya suka kai a Masallatai da wasu kasuwani da ‘yan arewacin Najeriya, ke gudanar da harkokin su a birnin na Aba.

Jami’an tsaron na kuma zargin mutanen da boye Boma-Bomai a sassa daban-daban da ‘yan arewacin Najeriya, ke gudanar da harkokinsu.

Mallam Bashir Idris, babban Limamin Masallacin juma’a na garin Aba, kuma daya daga cikin wadanda aka kama yace “ mu dai abunda ya bamu mamaki shine jami’an tsaro na soja sun yima diran mikiya tare da farma Masallacin, kan wani bincike Alhamdulillahi suka bincika basu sami koda reza ba, sun kuma shiga gida na da na Naibi na baa bun da suka samu sai suka koma sama makarantar yara inda ake koyarda Islamiya da kuma ilimin zamani anan suka shiga wani daki wanda ake binciken kimiya suka samu wasu ‘yan kwalabe shine suka tattara suka ce wai da shine muke hada boma-Bomai a Masallaci.”

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wannan lamari na dai zuwa ne a daidai lokaci da ‘yan arewcin najeriya dake zaman ci rani a jihar ta Abia ke zargin jami’an tsaro da gallazamasu, duk kokarin da wakilin mu yayi domin samun jami’an sojoji abun ya ci tura.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG