Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afurka Sun Bukaci Raba Rigakafin COVID Daidai-wa-daida


Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo Addo
Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo Addo

Shugabannin kasashen Afurka da dama ne suka yi jawabansu a rana ta biyu a taron kolin na Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai bayanan shugabannin sun fi maida hankali ne a kan batun coronavirus da batun raba rigakafin annobar daidai tsakanin kasashe.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta yace ya kamata batun tsara rabon rigakafi daidai wa daida a duniya ya zama babban abin da yaki da annobar zai fi maida hankali a kai muddun ana son duniya ta yi nasara a wannan yakin.

Shi ko shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo ya bayyana yanda annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin Afurka illa, ya ce sama da ‘yan Afurka miliyan 30 ne suka fada cikin tsananin talauci a shekarar 2020 kana wasu miliyan 40 kuma ka iya fadawa cikin talauci sakamakon annobar kana ya kwatanta tasirin cutar a kan Afurka da mai matukar muni.

Nana Addo ya ce ayyukan yi wajen miliyan 100 ne aka yi asarar su a Afurka. Ya ce mafita daya ita ce yi wa kimanin kashi 70 cikin 100 na al’ummar Afurka cikin dan lokaci kamar yanda aka yi a wasu wurare; don hakan zai taimaka ainun.

Kasar Peru za ta ayyana dokar ta baci a kan batun sauyin yanayi a kasar a kokarin bayyana himmarta a kan magance matsalolin sauyin yanayin, inji Shugaban kasar, Pedro Castillo, yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya.

Sarkin Saudi Arebiya Salman bin Abdulaziz al-Saud, ya fada a jawabinsa a taron na Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo cewa kasarsa tana bada muhimmanci ga zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaba, kana za ta taimaka a tattaunawar samar da zaman lafiya.

Sarkin Salman ya ce Saudi Arabia ta na son “samar da yanayi mai inganci ga ayyukan ci gaba kana da zarar an samu hakan za a cimma muradin al’ummar Gabas ta Tsakiya na samun makoma mai kyau.”

Sarkin Saudiyar ya yi alkawari cewa kasarsa za ta ci gaba da bada tallafin kasa da kasa duk da kalubalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta. Ya ce tuni kasar ta bada taimakon dalar Amurka miliyan 800 ga kasashe matalauta su yaki cutar COVID-19.

Ga rahoton Baba Yakubu Makeri daga birnin New York:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG