Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Zai Taimakawa Kamfanin ZTE Na China


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A wani yunkuri da ba saban ba Shugaba Trump ya bayyana anniyarsa na taimakawa domin farfado da kamfanin ZTE na China wanda ya kusa durkushewa saboda takunkumin da Amurka ta sa masa

Shugaban Amurka Donald Trump yace yana duba hanyar ganin kanfanin fasahan nan na kasar China ya koma bakin aikin sa cikin dan kankanin lokaci, bayan da dokokin kasuwancin Amurka suka durkusad da kanfanin

Dama Amurka ta yanke fitar da kayayyakin da kanfanin ZTE ke samarwa da wurin kashi 25 wanda kanfanin zaiyi anfani dashi wajen samar da wayoyin hannu, da sauran ayyukan da ya shafe shi.

Amurka ta dauki wannan matakin ne akan kanfanin na ZTE bayan an kama kiri-kiri tana anfani da fasahar Amurka wajen garwayawa da nata tana sayarwa kashen da Amuyrka tasa takunkumin kasuwanci , kasahen ko sun hada da Iran da Korea ta Arewa, inji wani masani harkokin fasaha.

Maaikatar cinikayya ta yanke damar da kanfanin na ZTE take dashi ne ga fasahar Amurka har sai zuwa shekarar 2025, wanda wannan ya tilasta kanfanin rufe masanaantar ta dake Shenzhen

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG