Shugaban darikar na duniya Shaikh Sheriff Muhammad Kabir Ibn Muhammad shi ya jagoranci sauran shugabannin darikar zuwa fadar shugaban kasar Najeriya.
Cikin tawagar akwai shugaban darikar na Najeriya Shaikh Ibrahim Dahiru Bauchi da suka gana da shugaban kasa Muhammad Buhari bayan sun kammala taronsu na kwana ukku da suka yi a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.
Malam Garba Shehu kakakin Shugaba Muhammad Buhari ya yiwa Muryar Amurka karin haske akan ziyarar shugabannin darikar Tijjaniya zuwa fadar shugaban kasa.
Inji Garba Shehu shugaban ya nuna masu cewar duk inda ake zaton tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya ya kai ya wuce nan. Gwamnatinsa ta gaji matsaloli da dama da suka hada da matsalar tsaro da Boko Haram ta haddasa da matsalar cin hanci da rashawa da ta yiwa kasar katutu. Haka kuma matsalar man fetur da mutanen yankin da ake hakoshi suke ganin nasu ne kuma sai yadda suka ga dama za'a yi dashi.
Shugaba Buhari ya nemi manya manyan malaman da suka ziyarceshi da su karfafa yiwa kasar addu'a kuma a yi kokarin shawo kan jama'a su fahimci cewa matsalolin da kasar ta tsinci kanta a ciki abubuwa ne da zasu wuce domin yanzu dole, kanwar naki, ta sa kasar ta fara fuskantar noma. Kasar ta fara maida hankalinta wajen ciyar da kanta da kuma samun arziki ta hanyar noma.
Dangane da cewa dama can akwai baraka tsakanin shugaban kasa da darikar saboda wai ya fi maida hankali akan darkar IZALA, kakakin ya musanta zargin yana cewa su basu san da wannan ba saboda shugaban kasa ya rungumi kowa da kowa.
Dan Shaikh Dahiu Bauchi wato Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana irin mahimmancin da suka baiwa ganawarsu da Shugaba Muhammad Buhari. Shugaban ya bukacesu su bayyanawa jama'a cewar kafin ya karbi mulki ana sayar da gangan mai daya dalar Amurka dari wani zibin ma fiye da haka amma sai gashi a nashi lokacin farashi ya fadi warwas inda gangan mai yanzu dala talatin da bakwai ne. Dalili ke nan da kasar ta samu kanta cikin wahala. Ko jihohi ma fiye da talatin basa iya biyan albashi. Ya kira a tsaya da addu'a.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.