Shugaban ya tura wata tawaga zuwa Borno a karkashin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Alhaji Abba Kyari da ministan tsaro da na yada labarai har da ma hafsan hafsoshin sojojin Najeriya da wasu jami'an tsaro.
Shugaban kasa ya aika da tawagar ne domin ta bayyana irin alhinin da yayi tare da juyayin abun da ya faru a garin Rann. Shugaban kasa ya kira duk 'yan Najeriya su tayashi yiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta'aziya.
Gwamnatin Buhari ta dauki alkawari yiwa wadanda suka jikata kowace irin jinya suke bukata kana ya bada tabbacin cewa rundunar sojojin kasar zata dinga kulawa sosai domin kaucewa irin kuskuren da ya faru.
A nashi jawabin gwamnan jihar Kashin Shettima ya nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya da kuma shugaba Muhammadu Buhari saboda damuwar da suka yi sanadiyar abun da ya faru a jihar. Gwamnan ya yi la'akari da tarihin yaki inda yace akan samu aukuwar irin abun da ya faru duk lokacin da ake yaki.
Tawagar ta ziyarci fadar mai martaba sarkin Dikwa inda suka jajanta masa gameda aukuwar lamarin saboda garin da abun ya faru na cikin masarautarsa. Daga bisani kuma sun ziyarci asibitin kwararru dake birnin Maiduguri.
Ministan tsaro Mansur Dan Ali dake cikin tawagar yayi karin haske inda yace har yanzu ba'a kammala tantance adadin wadanda suka ji rauni ba ko suka mutu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.