Shugaba Buhari yace duk wani fili da za'a iya yin shuka a kai a yi domin wadatar da kasa da abinci.
Shugaban yace ya yi magana da gwamnan babban bankin kasar da ministan noma akan lamarin da kuma " sarakuna yanzu". Shugaban ya cigaba da cewa zai yi magana da gwamnoni a koma noma ka'in da na'in.
Kalamun na shugaban kasa suna cikin abubuwan da ya fadawa sarakunan gargajiya a lokacin da yake bude baki dasu a fadarsa ta Aso Rock dake Abuja.
Ga masu nazari akan alamuran yau da kullum furucin shugaban na nuni da cewa ya fi son a cigaba da noma abinci a gida maimakon ya bude iyakoki domin a shigo da abinci, musamman ma lokacin da yace "na san bana an makara amma badi sai a daure a dage akalla "mu samu abun da zamu ciyar da kanmu"
Shugaba Buhari ya lissafa wasu kayan gona da kasar ta dogara dasu kafin a samu man fetur. Yace bayan samun man fetur din ne mutane suka bar noma, lamarin da yanzu ya zama wa kasar wani babban kalubale ga tattalin arziki sanadiyar faduwar farashinsa a kasuwannin duniya.
Dattawan arewa na neman a hada kai da kowane bangare domin dawo da zaman lafiya a Najeriya.
Alhaji Shehu Ashaka daya daga cikin dattawan yace shugaban kasa ya nemi 'yan siyasa ba masu nufin yin siyasa ba, a'aa, 'yan siyasa na gaske daga kowane bangare a yi magana dasu domin kasar ta zauna lafiya. Yace ba sojoji ba ne zasu kawo zaman lafiya, mutanen kasar ne zasu hada kansu su cimma matsaya domin zaman lafiya.
Ya kira shugaban kasa ya yi hakuri. Su ma 'yan siyasa su yi hakuri a zauna tare a ceto kasar daga masifar da ta shiga. A bar maganar jam'iyya.
Ga karin bayani.