Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KENYA: Jam'iyyar dake Mulki Ta Bukaci Kotun Kolin Kasar Ta Hukumta Madugun Adawa


Madugun adawa na Kenya, Raila Odinga,
Madugun adawa na Kenya, Raila Odinga,

Saboda madugun adawar Kenya ya ki shiga zaben da kotun kolin kasar ta ce a sake yi ya sa jam'iyyar dake mulkin kasar ta Kenya kiran kotun ta hukumta Raila Odinga

Jam’iyya mai mulki a Kenya, ta nemi wata kotu ta yanke hukuncin kin bin umurninta akan madugun ‘yan adawan kasar Raila Odinga, inda ta yi ikrarin cewa Odinga da magoya bayansa suna zagon-kasa ga zaben shugaban kasar da za a sake a makon da ke tafe.

Jam’iyyar ta Jubilee ta shigar da karar ne a gaban kotun kolin kasar a jiya Alhamis, yayin da Odinga ya tsaya tsayin-daka akan cewa shi da gamayyar jam’iyyu ta NASA ba za su shiga zaben ba wanda za a yi a ranar 26 ga watan Oktoban nan.

A cewar Odinga, hukumar zaben ta IEBC, ba ta shiryawa zaben ba, saboda haka, “a maimakon a yi wannan kwamacalar a barnatar da kudaden jama’a da lokaci, ya fi mana mu janye daga zaben,” kamar yadda shi Odinga ya fadawa manema labarai.

Sai dai kuma a jiya Alhamis, Sakatare-Janar na jam’iyyar Jubilee da ke mulki, Rapahel Tuju, ya ce har yanzu Odinga bai mikawa hukumar zaben wasikar janyewa ba.

A ranar 1 ga watan Satumban wannan shekarar ne, kotun kolin kasar ta Kenya, ta soke zaben farko da aka yi, tana mai cewa an tafka kurakurai a lokacin tattara kuri’u, hukuncin da ya soke nasarar da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta ya samu.

Kotun kolin ta bai wa hukumar zaben ta IEBC umurnin ta sake sabon zabe cikin kwanaki 60.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG