Mataimakiyar shugaban kasar Malawi ta bukaci a yiwa shugaban kasar Bingu wa Mutharika adu'a a saboda Alhamis din nan aka kai shi asibiti cikin gaggawa.
Kafofin diplomasiya sunce tunda farko Alhamis din nan shugaban dan shekara saba'in da takwas da haihuwa ya fadi, bayan daya kamu da ciwon zuciya.. Nan da nan dai gwamnati kasar Malawi bata fadi irin ciwon da shugaba yake fama dashi ba.
Kafofin kiwon lafiya, sunce yan sa'o'i kafin a kwantar da shugaban a asibiti ya suma. A wata hira da Muryar Amirka, mataimakiyar shugaban, Joyse Banda ta bukaci yan kasar Malawi da su hada kai su yiwa shugaban adu'a domin ya samu sauki ciki sauri.
Haka kuma Mrs Banda tace itama tayi rokon Allah ya bashi sauki, ya baiwa iyalin shugaban karfin jurewa da kuma kare su. Mrs Banda bada bada wani karin haske akan halin da shugaban yake ciki ba.
A shekara ta dubu biyu da hudu aka fara zaben shugaban, sa'anan kuma a lashe zabe a wa'adi na biyu a shekara ta dubu biyu da tara.
Masu caccakar manufofin gwamnatinsa, sunce shugaban yana kara zama mai mulkin kama karya. Mutane goma sha tara ne aka kashe a watan Yuli a lokacinda aka yi zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati