Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jan'iyun siyasar kasar Mali sun yi watsi da tayin gudanar da babban taron kasa


shugaban juyin mulki Amadou Sanogo
shugaban juyin mulki Amadou Sanogo

Manyan jami’yun siyasar kasar Mali sun yi watsi da kiran da shugabannin juyin mulkin sojin kasar suka yi, na gudanar da babban ‘taron kasa”

Manyan jami’yun siyasar kasar Mali sun yi watsi da kiran da shugabannin juyin mulkin sojin kasar suka yi, na gudanar da ‘taron kasa” da nufin shawo kan matsalolin siyasa da na tsaro da kasar ke fuskanta.

Gamayyar kungiyoyin siyasar ta FDR, da ta kunshi jam’iyun siyasa hamsin, ta bada sanarwar jiya Laraba cewa, taron ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Tun farko, shugaban juyin mulkin kyaftin Amadou Sanogo ya bayyana cewa, taron da ake neman gudanarwa da wakilan siyasa da na al’umma zai bada shawara kan matakan tunkarar kalubalai da kasar Mali ke fuskanta.

A halin da ake ciki kuma, jiya jumma’a sojojin juyin mulkin suka zargi ‘yan tawaye da keta hakin bil’adama a garin Gao. Garin na daya daga cikin garuruwa da dama a arewacin kasar, wadanda ‘yan tawayen azbinawa da mayakan kishin Islama suka kwace kwanan nan.

Sojojin sun ce an yi garkuwa da mata da kuma ‘yan mata a Gao, aka kuma yi masu fyade.

XS
SM
MD
LG