Kungiyar ta fitar da rahotonta ne a kan tambayoyi da ta yiwa ma'ikatan kiwon lafiya da wadanda suka shedi al'amarin tare da gudanar da wasu gwaje gwaje a inda aka kai harin a yankin Saraqeb dake gundumar Idilib
A wannan lokaci, kungiyoyin kiwon lafiya da wadanda suka fara bada bahasi, sun ce fararen hula sun nuna alamar sun shaki iskar Chlorine, suna fama da rashin nunfashi kuma ana jin warin Chlorine a cikin tafafinsu
Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta zargi rundunar shugaban Syria Bashar al-Assad da kai wannan harin guba a kan yankin da yan tawaye suke.
Kungiyar yaki da makamai masu gubar tace aikinta ne ta binciko ko yalla an yi amfani da makamai masu amma bata da alhakinta gano wanda ya kai harin.
Gwamnatin Syria ta sha musunta amfani da makamai masu guba a cikin yakin kasar da aka fara tun cikin watan Maris shekarar 2011.
Facebook Forum