Wasu takardu da aka gabatar a gaban kotu, su nuna cewa, Paul Manafort, wanda ya shugabanci kwamitin yakin neman zaben shugaba Trump na wasu watanni a shekarar 2016, ya bai wa wani abokin huldarsa mai alaka da jami’an leken asirin Rasha, bayanan da suka shafi ra’ayin jama’a kan gangamin yakin neman zabensu.
Wadannan bayanai sun kara kafa hujjar cewa mai yiwuwa kwamitn zaben na Trump, sun yi yunkurin hada wata alaka da Rasha a lokacin yakin neman zaben, koda yake, har yanzu masu shigar da kara basu kafa wata hujja da ta nuna haka ba.
A rahoton mai bincike na musamman Robert Mueller, ya tabbatar da cewar Manafort ya yi mishi karya a game da cewar akwai wani abu da aka yi musaya a tsakanin su da kasar Rasha.
Manafort, dai ya ki amincewa ko yana da wata alaka da mutumin nan da ake zargi Konstanti Kilimnik, dan kasar Ukrain wanda ke da alaka da kasar Rasha.
Facebook Forum