A jiya laraba shugaban kamfanin facebook Mark Zukerberg ya nemi gafara akan kuskuren da kamfanin yayi wajan kare bayanan mutane sama da miliyan hamsin dake amfani da shafin sa, yan kuma yi alkawarin daukar kwakkwaran mataki domin kare sake aukuwar hakan.
Katafaren kamfanin na ci gaba da fuskantar bincike daga gwamnatocin Amurka da na Burtaniya akan zargin da ake yi na bari shahararriyar cibiyar binciken harkokin siyasa ta yi amfani da shafin wajan daukar bayanan jama’a da ya taimaka wajan zaben shugaba Donald Trump a shekarar 2016. Amurka.
Ya ce “wannan ba karamin rauni bane daga gare ni, ina mai matukar bada hakuri, alhakin mu ne mu kare bayanan jama’a” a cewa Mark Zukerberg, shugaban kamfanin facebook, a wata hira da yayi da kafar yada labarai ta CNN.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin ya yi kwakkwaran bincike akan manhajojin kamfanoni da dama suke amfani da shafin wajan daukar bayanan mutane, da kuma daukar kwararan matakai wajan tabbatar da rashin sake aukuwar lamarin.
Koda shike shugaban ya bayyana cewa kamfanin bazai hana ko rage tallace tallace daga kamfanonin ba, amma zai tabbatar da kare bayanan jama’a, daga karshe ya bayyana farin cikin sa a gaban ‘yan majalisar Amurka, yayin da yake bayani kamar yadda suka bukaci yayi.
Facebook Forum