Gwamna Akpabio ya ce jam'yyarsu tana koina a kananan hukumomi 774 dake cikin Najeriya kuma ita ce kadai jam'iyyar da bata da wani uban gida. Ya yi hangen PDP zata taka rawar gani matuka a zaben shekara ta 2015. Ya ce PDP ta banbanta da duk wasu jam'iyyu kuma a hakikanin gaskiya 'yan Najeriya sun yadda da ita. Da zarar an sasanta matsalolin cikin gida da suka addabeta zata ba kowa mamaki.
Da aka ce ba ya ganin kawo sasantawar na daukan lokaci sai gwamnan ya ce a'a baya daukan lokaci. A dimokradiya dole a ba kowa zarafi ya fadi albarkacin bakinsa domin a cimma daidaituwa. Ya ce kuma ai mabiya bayan jam'iyyarsu suna nan daram. Ya ce bayan an daidaita zasu koma su fi da karfi sabo da ayyukan da jam'iyyar keyi. Ya ce a yi la'akari da ayyukan da gwamnatin Gombe keyi. Ya ce zai yi wuya wata jam'iyya ta yi tasiri a jihar Gombe.
Dangane da ganawarsu da gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dan Kwambo mai masaukinsa ya ce sun tattauna ne kan cigaban jihar kan abubuwan morewar rayuwar jama'a. Ya ce jihar Gombe tana da filin noma sabili da haka zasu hada hannu da jihar wurin aikin noma a matsayina na shugaban gwamnonin PDP. Ya ce zai hada kai da duk wanda yake son cigaba ta haka ne zasu ci nasara.
Ga karin bayani.