Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin PDP ka Iya Kaiga Gyara ko Rugujewa


Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo

Dimokradiya ta kunshi wani shirin gyaran kanka da kanka watakila abun dake faruwa ke nan a jam'iyyar PDP inji wani masanin ilimin kimiyar siyasa

Dr. Saidu Ahmed Dukawa masanin kimiyar ilimin siya ya ce ita dimokradiya nada wani abu wanda ke sa jam'iyya ta gyara kanta da kanta ko kuma ta ruguje gaba daya idan har rugujewanta ya zo.

Dr Dukawa ya ce watalila dayan biyu za'a iya kalli lamarin dake faruwa yanzu a jam'iyyar PDP. Tsarin dimokradiya nada wani al'amari na gyara kanka da kanka, wato kamar yana da karkuwar jiki wanda idan cututuka sun kawo masa farmaki ya ke gyara kansa da kansa. Babu abun mamaki watakila ita PDP din ce zata gyara kanta da kanta daga cikin fadi tashin da ta shiga. Abu na biyu kuma ba abun mamaki ba ne idan rugujewarta ce ta zo. Sabo da haka lamarin dayan biyu ne dole. Rigingimun na iya cigaba har sai PDP ta wargaje ko kuma ya haifar mata da gyaran dole.

Bisa ga wasikar da tsohon shugaban kasar Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban PDP na kasa Alhaji Bamanga Tukur Dr Dukawa, malami a Jami'ar Bayero ta Kano, ya ce watakila idan an samu gyara tsohon shugaban na iya cigaba da zama cikin jam'iyyar. Idan kuma gyara ya gagara babu mamaki ficewarsa ke nan.

Dangane da alfanun da jam'iyyar APC zata samu daga takaddamar, Dr Dukawa ya ce babban alfanu shi ne samun kariya gada zargin da PDP ta yi na kwana kwanan nan cewa jam'iyyar APC tana anfani da addini ko kuma ta Musulmai ce tsantsa. Idan hakan ya cigaba da faruwa mutane har ma da wadanda ba Musulmai ba zasu fice daga jam'iyyar su koma APC an karyata PDP ke nan.

Sai dai wani jigo a jam'iyyar PDP a Kano Alhaji Isa Dan Birni ya ce duk rubuce-rubucen da Obasanjo ya keyi bai kamata ba domin yana tsare wasu suka sha wahalar dawo da dimokradiya da wahalar kafa jam'iyyar kana da ya fito suka rungumeshi suka sa shi gaba har ya zama shugan kasa karo na biyu bayan wanda ya yi yana soja. Ban da haka kuma har ya zama shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar. Amma a ce yana rubuce-rubuce ya fadi wannan yau gobe ya fadi wancan ba daidai ba ne. Ya ce amma idan kaga mutum yana irin wannan maganar to yana son ya kama hanyarsa ne domin yan karo-karo sun kai masa ziyara har gidansa. Domin haka idan ya bari ya tafi PDP ba zata ce Iya ta gaida Aisha ba sai dai su na jira su ga menene zai faru a gaba.

Alhaji Murtala Sulengaro daya daga cikin wadanda suka shiga APC a cikin tawagar gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso ya ce Allah suke godewa da yake nunawa mutanen jihar Kano da mutanen Najeriya karara abubuwan da su sha fada. Mutane sun fitar da rai ko PDP zata yi masu aiki ko zata kaisu tudun mun tsira. Ya ce bayan Obasanjo duk manya-manyan kasar zasu fito su bi APC. Ya ce wannan shekarar shekara ce ta mamaki da mutanen Najeriya da jam'iyyar PDP zasu gani.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG