Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah wadai da harin da wata kungiyar ‘yan bindiga ta kai a Nijer, da ya rutsa da wasu ma’aikatan agaji na Faransa kana ya kashe akalla mutum takwas ciki har da mai musu rakiya da direban su.
Harin ya faru ne a wajen babban birnin kasar Yamai, a wani gandun namun daji da ya yi fice ga masu yawon bude ido. Wannan babbar kalubala ce ga Nijer, babbar abokiyar Amurka da sauran masu yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.
An hakikanta cewa, wannan ne harin farko da aka kai a kan ‘yan kasashen yammacin duniya a wannan yakin na Nijer,da ya kasance shahararren dandalin yawon shakatawa mai yawan rakumar dawa a kasar dake Afrika ta Yamma.
Da yake tattaunawa da Muryar Amurka a Dakar, Gilles Yabi, shugaban wata kungiyar mai suna WAHTI, dake daukar kanta wacce ta kware a harkokin al’ummar Afrika ta Yamma, ya ce wannan harin a yanki mai fama da rikici bai zo da mamaki ba, kasancewa an shafe shekaru ana fama da matsalar tsaro a kasashen yankin Sahel.
Facebook Forum