Dakarun tsaron Jamhuriyar Nijar da takwarorinsu na Barkhane sun fantsama cikin daji domin nemo ‘yan bindigar da suka aikata wannan mummunan kisan.
Yanzu haka jama’a a birnin Yamai na ci gaba da jimamin faruwar wannan al’amari saboda muninsa da kuma yadda ake ganin alamun yiwuwar ‘yan bindigar da suka aikata wannan ta’asa ba za su rasa masaniya ba game da zuwan wadannan turawan Nijar.
Mai sharhi akan sha’anin tsaro Alkassoum Abdourahamane ya sheda wa Muryar Amurka cewa "lamarin na bukatar samo amsar wasu tarin tambayoyi."
"Yadda aka yi suka samu labarin zuwan wadannan mutanen har suka riske su suka aikata wannan mummunan aiki, akwai alamun cewa wasu suka ba su cikakken bayanai akan hakan," in ji Abdourahamane.
Duk da cewar har yanzu ba a tantance ainihin inda maharan suka fito ba masana na cewa ba mamaki kungiyoyin ta’addancin arewacin Mali ke da alhakin wannan aika aika.
Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou a shafinsa na Twitter ya yi Allah wadai da faruwar abin da ya kira danyen aiki yayin da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ya ce ‘’an yi wa kasashenmu illa amma kuma jajircewarmu akan maganar murkushe kungiyoyin ta’addanci ta na nan daram saboda haka yaki yanzu aka fara.’’
Bayanan safiyar yau Litinin na cewa tuni aka iso da gawarwakin wadannan mamata a Yamai inda ake shirin kai su kasar Faransa.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti.
Facebook Forum