Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Banglades Na Rikon Kwarya Ya Yi Kiran Da A Kai Zuciya Nesa


BANGLADESH-POLITICS-UNREST
BANGLADESH-POLITICS-UNREST

Yunus mai shekaru 84, da ya taba lashe lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi, da ke fuskantar babban kalubale na kawo karshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen demokradiyya.

A jiya Assabar shugaban rikon kwarya na Bangladesh Muhammad Yunus ya yi kira ga samun hadin kan addinai bayan ganawa da mahaifiyar dalibar da 'yan sanda suka harbe har lahira, lamarin da ya janyo zanga-zangar da ta kawo karshen mulkin Sheikh Hasina na tsawon shekaru 15.

Yunus mai shekaru 84, da ya taba lashe lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi, da ke fuskantar babban kalubale na kawo karshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen demokradiyya.

Ya shaida wa manema labarai cewa "Hakinmu shi ne gina sabuwar Bangladesh,"

Hare-haren ramuwar gayya da aka kai kan mabiya addinin Hindu tsiraru a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin Hasina, ya haifar da fargaba a makwabciyar kasar Indiya da kuma fargaba a cikin gida.

A yayin wata ziyara da ya kai birnin Rangpur da ke arewacin kasar, Yunus ya yi kira da a kwantar da hankali, ta hanyar tunawa da karrama Abu Sayeed, dalibi na farko da aka kashe a rikicin na watan jiya.

Muhammad Yunus, Shugaban Rikon Kwarya Na Banglades
Muhammad Yunus, Shugaban Rikon Kwarya Na Banglades

Ya kara da cewa "Abu Sayeed yanzu yana cikin kowane gida, yadda ya tsaya muma haka muke yi". "Babu bambance-bambance a Bangladesh ta Abu Sayeed."

A ranar 16 ga watan Yuli ne ‘yan sanda suka harbe Sayeed, mai shekaru 25, sa’adda ‘yan sanda suka fara kai farmaki kan masu zanga-zangar da dalibai suka jagoranta ta kin jinin gwamnatin Hasina.

Hasina, mai shekaru 76, ta fice daga kasar da jirgin sama mai saukar mai saukar ungulu zuwa makwabciyar kasar Indiya a ranar Litinin, yayin da masu zanga-zangar suka mamaye titunan Dhaka a wani gagarumin yunkurin kai karshen mulkinta.

Ana zargin gwamnatinta da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan gillar da aka yi wa dubban abokan hamayyarta na siyasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG