Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Yace Kisan Gillar Orlando Mai Tsatsauran Ra'ayi Ne Ya Aikatashi


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barrack Obama ya fada jiya Talata cewa kisan gillar nan da aka yi a Amurka mafi muni, wani matashi ne ya aikata shi wanda yake mutum ne mai tsatsauran ra'ayi.

Obama yace kawo yanzu masu bincike basu samu ko wani dalili dake danganta makashin da wata kungiyar ta'adda daga kasar waje ba.

Yace shi wannan saurayin Omar Saddiqui Mateen haifaffen musulmin Amurka ne, dan shekaru 29 da haihuwa, ya aikata wannan aika-aikan ne ranar Lahadi a gidan shakatawar yan kungiyar ma'aurata jinsi guda, wato, masu ludu da madigo dake birnin Orlando dake jihar Florida ta nan Amurka.

Mateen dai ya samu nasarar kashe mutane har 49 kana ya jima 53 rauni, wadanda 6 daga cikin su suna nan ga ALLAH rai kwakwai-mutu-kwakwai.

A cikin jawabin da shugaba Obama yayi bayan taron inganta matakan tsaro tare da duba abinda ya faru a birnin na Orlando da kokarin da kuma Amurka keyi na ganin ta durkusad da kungiyar ISIS a kasashen gabas ta tsakiya, Obama yace Mateen ya samu wannan mummunar akida ce ta anfani da hanyar sadarwan yanar gizo ko internet.

Shugaba Obama yace jami'an tsaron Amurka na nan na iya bakin kokarin su domin ganin sun dakile aukuwar irin wannan al’amari, Sai Obama ya bayyana irin wahalar dake tattare da gano ire-iren wadannan mutanen kafin su kai ga aikata wannan ta'asar.

Sai dai tun farko Babban jamiin tsaron cikin gida Chief Jeh Johnson ya kira da a samar da dokar mallakar bindiga barkatai, sakamakon ganin abinda ya faru a Orlando.

Yace yanzu haka dai mahukunta na nan na cigaba da tattara bayanai game da rayuwar shi Mateen.

XS
SM
MD
LG