Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Mika Alhininsa Ga Mutanen Orlando


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce babu wata kwakwarar hujja da ke nuna cewa dan bindigar nan da ya halaka mutane a kisan-kiyashi mafi muni a kasar a gidan rawa na ‘yan luwadi da ‘yan madugo a Orlando a Jihar Florida, ya samu umurni ne daga wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke ketare.

Ga dukkan alamu, a cewar Obama, yayin da ya ke ganawa da ‘yan jarida a Fadar White House, dan bindigar ya samu bayanai ne daga wadanda ake wallafa a kafar internet.

Obama ya ce, dan bindigar mai suna Omar Saddiqui Mateen mai shekaru 29, wanda kuma aka haifa anan Amurka da iyayensa ‘yan asalin Afghanistan, misali ne na irin ‘yan ta’adda na cikin gida da suke yawan nuna damuwa akansu.

Amma kuma ga dukkan alamu, ya nuna mubaya’arsa ga kungiyar IS a lokacin da ya kira lambar neman daukin gaggawa ta 911.

Fadar White ta sanar da cewa a ranar Alhamis Shugaba Obama zai kai ziyara zuwa birnin na Orlondo.

“ Wannan mummunan hari ne akan Amurkawa, wanda ya kasance mai cin rai musamman ga al’umar Orlando, amma mu san cewa, haka kan iya faruwa a ko’ina a kasar nan, kuma muna goyon bayan al’umar Orlando muna kuma taya iyalan wadanda harin ya rutsa da su alhini.”

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG