Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yemen 'Yan Houthi Sun Kame 'Yan Sunni 120


'Yan Tawayen Houthi
'Yan Tawayen Houthi

Duk da tayin tattaunawar zaman lafiya da Houthi suka yi sun kame 'yan sunni 120

‘Yan tawayen Houthi masu bin darikar Shia a Yemen sun kama mutane 120 ‘yan darikar Sunni duk da tayin tattaunawar zaman lafiya da shugaban Houthi din ya yi.

‘Yan Houthi sun kai samame a gidaje da ofisoshi a babban Birnin kasar Sana’a suka kame ‘yan jam’iyyar Islah wadda take da alaka da kungiyar 'Yanuwa Musulmi ta kasar Masar. Islah tana goyon bayan hare-haren da Saudiya da kawayenta ke kaiwa kan ‘yan Houthi.

‘Yan Houthin sun kai samamen ne yayinda shugbansu Saleh al-Sammad yace ‘yan tawayen ashirye suke su fara tattaunawa domin samun zaman lafiya idan Saudiya zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kansu.

Sammad ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters jiya Lahadi cewa “bamu da wasu sharruda illa a daina kai mana hare-hare kuma duk kasar da bata tsangwama mana tana iya shiga tattaunawar.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Yemen ko kuma daga wasu kungiyoyi masu hamayya. Amma can baya duk kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na kawo daidaituwa ya cutura

XS
SM
MD
LG