Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Donald Trump Ya Kammala Ziyarar da Ya Kai Nahiyar Asiya


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya kammala ziyarar kwanaki 12 a kasashe biyar na yankin Asiya, wanda batun barazanar shirin Nukiliyar Koriya ta Arewa da bunkasar harkokin cinikayya suka mamaye ta.

Bayan tattaunawar da ya yi a Manila jiya Litinin, tare da Fara Ministotin Australia da Japan, Trump yayi alkawarin zai gabatar da wata babbar sanarwa akan Koriya ta Arewa da kuma harkokin cinikayya idan ya dawo nan Washington a wannan makon. Amma bai bayar da cikakken bayani kan sanarwar ba.

A halin da ake ciki kuma, wata kafar yada labaran Amurka ta fitar da rahotan da ke cewa shugaba Trump ya bukaci takwaran aikin sa na kasar China Xi Jinping da ya sa baki a maganar kama wasu ‘yan wasan kwalon Kwandon Amurka daga jami’ar California UCLA, wadanda aka kama da laifin sata a makon da ya gabata a birnin Hangzhou.

Trump dai ya tabo wannan batu ne yayin da yake tattaunawa da Xi Jinping a ranar Asabar a Beijing, inda shugaban na China ya yi masa alkawarin cewa, za a yiwa ‘yan wasan adalci ba tare da bata lokaci ba, a cewar jaridar The Washington Post.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG