Shugaban Amurka Donald Trump, jiya Jumma'a ya sake barazanar rufe kan iyakar Amurka da Mekziko (Mexico) kwata-kwata, tare kuma da katse tallafin da Amurka ke baiwa kasashen Honduras da Guetemala da kuma el-Salvador, muddun Majalisar Dokokin Taryyar Amurka ta ki tanadar da kudin gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico.
A wasu jerin sakonnin twitter da ya tura, Trump ya yi kiran da a canza abin da ya kira dokokin shigi da ficin Amurka na shirme, wadanda su ka zama matsala ga Amurka.
Wadannan kalaman na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta shiga rana ta 7 a jere, da wasu sassan gwamnatin tarayya su ka kasance a rufe saboda rigimar kasafin kudi tsakanin Trump, wanda ke son a tanaji dala biliyan 5 don gina katanga, da kuma 'yan Democrat masu goyon bayan samar da kudi kalilan, kuma su ke matukar adawa da batun gina katangar.
Facebook Forum