Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Da Kim Sun Isa Singapore


Shugaba Donald Trump Kan hanyar zuwa Singapore
Shugaba Donald Trump Kan hanyar zuwa Singapore

Shugaban Donald Trump ya isa kasar Singapore domin taron koli da takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa Kim Joung Un, ganawar da Amurka tace, yana da kyakkyawan kwarin guiwa a kai.

Ministar harkokin kasashen ketare na kasar Singapore Vivian Balakrishnan ne ya tarbi shugaba Trump lokacin da ya fito daga jirgin shugaban kasan amurka Air Force One yau Lahadi.

Kafin isarshi wurin taron yau lahadi, Trump ya kuma bayyana cewa, yana kan hanyar shiga wani bangare da ya zama bako a gareshi, domin ganawar ranar Talata.

Da yake amsa tambayar Muryar Amurka kafin tashi zuwa Asiya daga wurin taron kolin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G7, shugaba Trump yace, “ina da kwarin guiwa sosai” a kan ganawa tsakanin shugaban Amurka mai ci da dan iyalin masarautar da take mulkin kama karya a daya daga cikin kasashen da aka fi mayarwa saniyar ware a duniya na tsawon zuri’a uku.

Trump yace ya hakikanta Kim, wanda shekarunsa basu kai rabin na shugaban Amurka ba, “yana so ya yi wani abu mai tasiri ga al’ummarshi” Sai dai Trump ya yi gargadi da cewa, Kim “ ba zai sake samun wannan damar ba” idan kwalliya bata biya kudin sabulu a tattaunawar ba- tare da bayyana wannan damar ta bin matakan diplomasiya da Amurka a matsayin dama ta farko kuma ta karshe.”

Kim ya isa Singapore yau da rana, yayinda ake ta kila wakala kan sakamakon tattaunawar da za a yi ranar Talata.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG